Za a janye jirgin ruwan Costa Concordia

Jirgin ruwan Costa Concordia a kasar Italy
Image caption Jirgin ruwan Costa Concordia a kasar Italy

A ranar Lilitinin ne za a fara aikin dago jirgin ruwan yawon shakatawar nan, Costa Concordia a gabar tekun kasar Italiya.

Wannan shi ne aikin ceto mafi girma da aka taba yi a gabar tekun kasar, yayin da ma'aikatan ceton ke kokarin dago jirgin na Costa Concordia, da ya yi hatsari a bara.

An dai daura manyan sarkokin karfe da wayoyi a jikin jirgin, wanda ke jirkice a cikin ruwan.

Burin dai shi ne na a birkito wannan katafaren jirgin, ta yadda za a iya tunkuda shi zuwa gaba.

Mahukuntan kasar ta Italiyar sun ce za a fara aikin dago jirgin ruwan, bayan ya hatsarin da ya yi a bara.