Wutar lantarki ta kashe mutane 6 a jihar Kebbi

Tashar samar da wutar lantarki a Najeriya
Image caption Tashar samar da wutar lantarki a Najeriya

Mutane shida sun rasa rasu sakamakon hatsarin wutar lantarki da ya abku a karamar hukumar Jega dake jahar Kebbi arewacin Najeriya .

Wani mazaunin garin na Jega ya shaidawa BBC cewa lamarin ya abku ne a daren jiya, bayan an dawo da wutar lantarki da karfi, da yasa duk abinda mutum ya taba sai karfin wutar lantarkin ya ja shi.

Duk da cewa ba kasafai akan samu irin wannan hatsari ba, amma kuma yawan daukewa da kuma dawo da wutar lantarkin a Najeriyar kan haifar da barazana abkuwar gobara a lokuta da dama.