'Yan Nijar sun soki shigar Mangal harkokin kasar

Kamfanin uranium na Nijar
Image caption MNSD ta zargi gwamnatin Nijar da yin huldar kasuwancin da ta saba ka'ida tsakaninta da Mangal

A Jamhuriyar Nijar, wasu 'yan jam'iyar adawa ta MNSD Nasara na suka game da rawar da hamshakin dan kasuwan Najeriya, Alhaji Dahiru Mangal ke takawa a harkokin tattalin arzikin Nijar.

Jam'iyyar ta zargi Mangal da yin kane-kane a fannin man fetur da ma'adanin uranium, abubuwan da yakamata ace 'yan kasar Nijar ne a kai.

Haka kuma jam'iyyar ta zargi Mangal da yin katsalanda a cikin harkokin siyasar kasar.

Sai dai wasu mukarrabansu sun musanta zarge-zargen, suna mai cewa babu inda Mangal ya hana ruwa gudu.