Za a yi zaben majalisar dokoki a Rwanda

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame
Image caption Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame

Al'ummar kasar Rwanda za su kada kuri'a, domin zaben wadanda za su wakilce su a majalisar dokokin kasar.

Hukumomi sun ce babu makawa za a gudanar da zaben, duk da damuwa kan harin da aka kai a birnin Kigali, a karshen mako da ya yi sandiyyar mutuwar mutane biyu.

Jam'iyun siyasa hudu da kuma 'yan takara masu zaman kansu hudu ne, za su fafata kan neman kujeru 53 na majalisar dokokin kasar.

Wasu masu sharhi kan al'amuran siyasa sun ce har yanzu akwai jan aiki a gaban 'yan majalisar dokokin Rwandar wajen yin fafitikar dakile yin katsalandan daga mahukuntan kasar ke yiwa harkokin majalisar.