Tarayyar Turai za ta ba Somalia Euro 650m

Shugaban Somalia da shugaban majalisar tarayyar Turai
Image caption Manufar sabuwar yarjejeniyar ita ce baiwa kasashe masu rauni karin iko, wajen biyan bukatun su na cigaba

Kungiyar tarayyar Turai ta yi alkawarin ba da euro miliyan 650, a taron da ake yi na taimaka wa Somalia a Brussels.

Kudin dai wani bangare ne na 'sabuwar yarjejeniyar' ga kasar da ake yiwa kallon ta ruguje.

Wakilan kasashen duniya da kungiyoyin bada agaji da kuma cibiyoyin kudade, ne su ke halartar taron.

Shugaban Somaliya Hassan Sheik Mahmud ya jinjinawa yunkurin na sabuwar yarjejeniyar, amma kungiyar masu fafutukar Islama ta Al Shabab ta yi watsi da shi a matsayin bata lokaci.