An yi amfani da makami mai guba a Syria

Ban Ki moon, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya
Image caption Ban Ki moon, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Masu binciken makamai na majalisar dinkin duniya sun ce, an yi amfani da makami mai guba yayin harin da aka kai a kusa da Damascus, babban birnin Syria, a ranar 21 ga watan Agusta.

Sakatare janar na majalisar ta dinkin duniya, Ban Ki Moon, ya ce rahoton masu binciken makaman yana da tada hankali sosai, kuma ya bada hujjoji masu karfi da ke tabbatar da cewa, an yi amfani da makami mai guba.

Ban Ki Moon ya ce, gwajin kasar wurin da aka kai harin na nuna cewa an yi amfani da gubar Sarin, kuma su ma rokokin da aka yi amfani da su a wurin suna kunshe da gubar Sarin.

Duk da cewa rahoton binciken bai ce komai ba a kan batun ko wanne bangare ne yayi amfani da makami mai guba, amma rahoton ya ce 'yan tawayen Syria basu da irin rokokin da aka yi amfani da su wajen kai harin.

Mr Ban yace kasashen duniya suna da nauyi da ya rataya a wuyansu na ganin an gurfanar da wadanda suka aikata wannan ta'asa.

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius, shine na farko da ya mayar da murtani.

Ya ce rahoton masu binciken ya nuna ba makawa gwamnatin shugaba Assad ce ke da alhakin hakan.