An tilasta wa mace cire nikabi a kotun London

Image caption Matar a kan harabar kotun a London

Wani alkali a Birtaniya ya yanke hukuncin cewa tilas ne wata mata Musulma dake gurfana a gaban kotu a London ta yaye nikabin dake rufe fuskarta, idan za ta bayyana a gaban kotun.

Yana cewa rufe fuskar ruf bai dace da tsarin shari'ar da ake yi ta komai a fayyace ba.

Matar mai shekaru ashirin da biyu ta gurfana a gaban kotun ne da nikabi , ana zarginta da laifin razanaswa.

Shi ne alkalin ya ce akwai bukatar ya kalli fuskarta, domin ya fahimci inda ta sa gaba.

'Tsarin addinni'

Alkalin ya jadadda cewar zai iya baiwa matar wani abu da zai kare fuskarta yadda jama'a ba za su ganta ba, amma dole ne shi da lauyoyi su ga fuskar.

A cewarsa, nan gaba a ci gaban shari'ar za ta iya dunga lullube fuskarta.

Kawo yanzu dai matar ta ki bin amurnin alkalin na cire nikabin, inda ta ce addininta ya bata 'yancin ta rufe fuskarta a inda maza suke.

Idan har matar ta ki amincewa da umurnin kotun, za a daure ta a gidan kaso bisa laifin raina kotun.