Kotu ta umarci wata ta cire nikabinta

Wata mata Musulma sanye da niqabi
Image caption Wata mata Musulma sanye da niqabi

Wani alkali a Birtaniya ya yanke hukuncin cewa tilas, wata mata Musulma wacce aka gurfanar a gabansa a London, ta cire nikabin dake fuskarta.

Alkalin na cewa rufe fuskar ruf bai dace da tsarin shari'ar da ake yi ta komai a fayyace ba, kuma yana bukatar ganin fuskarta, domin ya fahimci inda ta sa gaba.

Matar mai shekaru 22 ta gurfana a gaban kotun ne da nikabi, kuma ta musanta zargin razanarwar da ake mata.

Lauyoyinta sun ce tilasta mata bude fuskarta, ya keta hakkinta na dan Adam.