PDP: Baraje ya ziyarci Majalisar Dokoki

Image caption Wasu 'yan majalisar Najeriya na son a cire takwarorinsu da basa goyon bayan Baraje

A Najeriya, yayin da 'yan majalisun dokokin tarayya suka koma bakin aiki ranar Talata, shugaban 'sabuwar PDP', Abubakar Kawu Baraje, ya kai wa 'yan majalisar ziyara.

Ziyarar dai tana da dangantaka da rabuwar da jam'iyyar PDP ta yi inda wasu gwamnoni da jiga-jiganta, ciki har da 'yan majalisun dokokin suka balle.

Wasu 'yan majalisar dai sun bijirewa yunkurin hana Alhaji Baraje shiga majalisar, sai dai wasu sun goyi bayan shigarsa, suna masu cewa kotun kasar ma ta amince da kasancewarsa shugaban wani bangare na jam'iyar ta PDP.

Wasu 'yan majalisar dai sun shaidawa BBC cewa suna so su cire wasu daga cikin jagororin majalisar wadanda suke gani ba sa tare da bangaren Alhaji Baraje.

Karin bayani