Kwamitin sulhu na taro kan Syria

Zaman Kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya
Image caption Kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya

Kasashe biyar dake da kujerar dindindin a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya suna taro a birnin New York inda suke tattauna daftarin wani kuduri akan batun Syria.

Amurka, da Faransa da kuma Birtaniya ne suka gabatar da kudurin domin fayyace yadda za'a aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Amurka da Rasha akan lalata makamai masu guba da Syria ta mallaka.

Sai dai kuma akwai sabani akan ko kudirin da za'a gabatar zai hada da batun daukar matakin soja akan Syria:

Tun farko dai ministocin harkokin wajen Faransa da Rasha sun kasa cimma daidaito a kan wanda ya kamata a dorawa alhakin kai hari da makami mai guba a Syria.

Bayan tattaunawarsu a Moscow, Laurent Fabius na Faransa ya ce rahoton Majalisar Dinkin Duniya a kan lamarin na watan Agusta ya nuna tabbas cewar gwamnatin Syria ce keda alhakin kai harin.

Amma takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov ya ce Moscow ta yi ammana cewar dakarun 'yan tawaye ne suka kadammar da harin.

Mr Fabius na matsin lamba ga Rasha don ta goyi bayan kudurin kwamitin tsaro a kan daukar mataki mai tsauri a kan Syria.

'Binciken kwararru'

A ranar Litinin, masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun ce an yi amfani da sinadari mai guba 'sarin' a kan fararen hula a ranar 21 ga watan Agusta a Damascus.

Sakatare Janar na Majalisar, Ban Ki-moon ya bayyana harin a matsayin laifi na yaki.

Gwamnatin Amurka na zargin gwamnatin Syria da laifin hari da makami mai guba abinda kuma janyo barazanar daukar matakin soji.

A karkashin yarjejeniyar wacce Rasha da Amurka suka amince, Syria za ta bayyana yawan makamanta masu guba cikin mako guda sannan a lalata su daga nan zuwa tsakiyar shekara ta 2014.

Karin bayani