'Zamu ci gaba da kwace kamfanonin turawa'

Image caption Shugaba Robert Mugabe

Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya sha alwashin ci gaba da shirinsa na kwace kamfanonin 'yan kasashen waje su koma mallakar 'yan kasa.

A jawabinsa wajen bude sabuwar majalisar dokokin da aka zaba a watan Yuli, Mr Mugabe ya ce babu gudu babu ja-da baya a wajen aiwatar da shirin.

Jam'iyyar adawa ta MDC ta kauracewa zaman majalisar.

A shekara ta 2010 ne aka fara aiwatar da dokar mallakar kamfanoni inda 'yan kasashen wajen za su baiwa 'yan Zimbabwe kashi 51 cikin 100 na hannun jarin kamfanoninsu.

Masu suka sun ce matakin zai hana masu zuba jari shiga cikin kasar.

Karin bayani