Shugabar Brazil ta soke ziyara zuwa Amurka

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff

Shugabar Brazil Dilma Rousseff, ta soke wata ziyara data tsara kaiwa Amurka a wata mai zuwa saboda dazarge zargen leken asiri.

An zargi hukumar leken asirin Amurka da duba sakonnin email, da wasu bayanai na dubun dubatar 'yan kasar Brazil.

Sun kuma hada da masu yiwa Ms Rousseff hidima, da kuma bayanan jami'an kamfanin man Kasar na Petrobas.

Wannan badakala dai , ta harzuka 'yan Brazil. A wata sanarwa gwamnatin Brazil din tace shugabar ba zata iya kai ziyarar ba, har sai an gudanar da wani cikakken bincike.