An ceto mace bayan kwanaki 15 a rijiya

Image caption Wani yaro da aka taba tsamowa a wata rijiya a China

Kafar yada labaran gwamnati a China ta ce an ceto wata mata data makale har tsawon kwanaki goma sha biyar a cikin wata rijiyar da ba a amfani da ita.

Matar mai suna Su Qixi, ta shafe wadannan kwanaki ne a raye cikin rijiyar, tana shan ruwan sama da kuma cin masarar dake hannunta a lokacin data fada cikin rijiyar.

Wasu kauyawa ne dai suka gano ta, bayan sun ji tana ihun a zo a taimake ta.

An dai ce matar tana asibiti yanzu haka, amma bata cikin mawuyacin hali.