Za a tura sojoji zuwa Nassarawa

Image caption Dakarun Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bada umurnin a tura dakarun soji a jihar Nassarawa dake fama da rikicin kabilanci.

Kakakin rundunar soji, Birgadiya Janar Ibrahim Attahiru wanda ya bayyanawa manema labarai hakan, yace sojojin za su hada hannu da 'yan sanda wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

A karshen mako ne rahotanni suka nuna cewar an kashe fiye da mutane hamsin a tashin hankalin kabilanci da aka yi a jihar ta Nassarawa tsakanin 'yan kabilar Eggon masu rinjaye da kuma 'yan kabilar Alago wadanda tsiraru ne.

A watan Mayun da ya wuce ne, wasu 'yan kungiyar asiri na kabilar Eggon wadanda ake kira 'Ombatse' suka yi wa jami'an tsaron Najeriya kwantar bauna suka kashe akalla jami'an 65.

Karin bayani