An soma shari'ar Saif al-Islam a Libya

Image caption Saif al-Islam

An soma zaman farko na shirye shiryen fara shara'ar dan marigayi Kanar Gaddafi, Saif al-Islam da kuma shugaban hukumar leken asirinsa, Abdullah al Senoussi a Tripoli babban birnin Libya.

Za a gabatar da tuhumar da ake yi wa mutanen biyu da sauran tsaffin jami'an Kanar Gaddafin, wadda ta hada da kisan kai a lokacin boren da ya kai ga hambarar da Shugaban na Libya a 2011.

Ana tsare da Seif al-Islam ne a garin Zintan tun lokacin da aka kama shi, rundunar sojin da take tsare da shi ta ce dalilan tsaro sun hana kai shi Tripoli.

Ya bayyana a wata kotu a Zintan da safiyar ranar Alhamis a wata shara'ar ta daban, wadda aka dage har zuwa watan Disamba.

Karin bayani