An kashe mutane casa'in a Beni Sheik

Wani sojan Najeriya a Baga
Image caption Akwai rahotannin kashe wani soja da matar wani jami'in 'yan sanda a wani kauye dake yankin

Jami'ai a Najeriya sun ce an kashe kusan mutane 90, a wani harin da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram da kaiwa kan wani kauye a arewa maso gabashin kasar.

Lamarin ya faru ne a kauyen Benisheik na jahar Borno, inda mayakan sanye da kayan soji, sun shiga kauyen suka kokkona dimbin gidaje.

Haka ma rahotanni sun ce sun kuma kakkafa shingayen binciken ababen hawa, a kan wata babbar hanya inda suka kashe mutane masu yawa da ke wucewa.

A ranar Laraba sojan kasar sun ce sun kashe sama ga mayakan kungiyar su 150, a wani farmaki da suka kai kan wani sansaninsu.

Karin bayani