Rouhani ya yi tayin sa baki a Syria

shugaban Iran Hassan Rouhani
Image caption Ana sa ran Obama zai gana da Rouhani a lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya mako mai zuwa.

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya nuna aniyar gwamnatinsa ta taimaka wa wajen tabbatar da zaman lafiya a Syria.

A abin da ya kira manufarsa ta tattaunawar ci gaba da sauran kasashe.

A wata kasida da ya wallafa a jaridar Washington Post.

Mr Rouhani ya bukaci kasashen duniya su yi amfani da zabensa tare da Iran su kawo karshen gabar da ke ruru wutar rikici a Gabas-ta-tsakiya.

Jami'an fadar gwamnatin Amurka sun ce a shirye Shugaba Obama yake ya gana da Mr Rouhani.