Kungiyar kare muhalli ta zargi Rasha

alamar kamfanin iskar gas na Rasha Gazprom
Image caption Wasu 'yan kungiyar kare muhallin sun yi yunkurin kawo cikas ga aikin kamfanin ranar Laraba.

Kungiyar yaki da gurbata muhalli ta Greenpeace ta ce wasu 'yan Rasha sun yi wa daya daga cikin jiragen ruwanta dirar mikiya suka ritsa jami'anta da bundugogi.

Jirgin yana wani yanki ne na tekun Arctic na kasashe a wani mataki na adawa da aikin hakar iskar gas da kamfanin gas na Rasha Gazprom yake yi.

Wani daga cikin 'yan kungiyar ya sheda wa BBC kimanin mutane 15 ne da suka rufe fuskokinsu suka dirar wa jirgin daga wani jirgin sama mai saukar ungulu.

Kungiyar ta Greenpeace ta yi imanin cewa mutanen jami'an hukumar tsaro ta cikin gida ta Rasha ne.