An hana askar tsare mata masu tuki a Saudiyya

Image caption Mata zasu shiga mota a Saudi Arabia

Rahotanni daga Saudi Arabia sun nuna cewar an bayyanawa askar a kasar sun daina tsare mata masu tuka mota.

Jaridar Al Hayat ta Saudiyya ta ambato wasu majiyoyi a hukumar tabbarda da'a, na cewar kada ma'aikata su wuce gona da iri wajen hukunta mata masu tuka mota.

Mata ba sa tuka mota a Saudiyya duk da cewar babu wata doka da ta haramta musu.

Masu rajin ganin kare 'yancin mata wajen tuka mota sun kaddamar da kampe a shafin Twitter, inda suka bukaci mata a Saudiyya su fito ranar 26 ga watan Okotoba su tuka mota a fadin kasar.

Karin bayani