Hudubar Juma'a kan 'ya'ya mata a Pakistan

Image caption Ilimantar da mace tamkar ilmantar da al'umma ne

An bukaci Limamai a masallatan Juma'a a ko'ina cikin Pakistan da su yi huduba a kan kula da 'ya'ya mata.

Majalisar Limamai ta kasar tana fatan cewar har kashi 70 cikin 100 na masallatai ne za su shiga cikin abinda ta kira ranar da suka lakantawa ta "Diya ta albarka ce, ba sharri ba".

Wata marubuciya 'Yar Pakistan, Binah Shah ta shaidawa BBC cewar malaman addini dake cikin al'umma nada muhimmiyar rawa da za su taka wajen ilmantar da jama'a su kara mutunta 'yan mata.

A cikin 'yan kwanakin nan dai lamura da yawa sun janyo hankali jama'a, musamman jefa wata yarinya yar shekara daya da rabi da mahaifinta yayi cikin kogi saboda abunda aka yi zargin yana son da namiji ne.