Syria ta fara ba da bayanai kan makamanta

Image caption Ana sa ran kammala lalata makaman Syria kafin karshen 2014

Gwamnatin Syria ta fara mika cikakkun bayanai kan makamanta masu guba ga hukumar da ke fafutikar ganin an kawar da makamai masu guba ta duniya da ke birnin Hague.

Kakakin hukumar ya ce sun karbi bayanan farko kan makaman masu guba, yana mai cewa suna sa ran za su karbi bayanai da dama nan gaba.

A karkashin yarjejeniyar da Amurka da Rasha suka amince da ita, ana sa ran Syria za ta kammala mika makamanta masu guba ranar Asabar.

An yi amannar cewa Syria tana da ton 1,000 na makaman masu guba.

Ana sa ran za a lalata makaman nata daga yanzu zuwa tsakiyar shekara mai zuwa.

Karin bayani