'Kisan gillar' Abuja ya bar baya da kura

Image caption Shaidu sun ce ko baya ga mutuwar mutane 6, wasu kuma 12 sun samu raunukka.

An samu bayanai masu karo da juna dangane da gaskiyar abin da ya faru a wani gida da ke unguwar Apo a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja inda aka yi harbe-harbe da tsakar daren juma'a.

Hukumar 'yansandan ciki wato SSS ta kasar dai ta ce sojoji sun yi musayar wuta da mayakan kungiyar Boko Haram ne lokacin da suka kai sumame a gidan garin neman makamai; abin da yayi sanadiyar raunata wasu.

Sai dai mazauna gidan sun ce babu wanda ke da makami a cikinsu illa jami'an tsaron ne suka bude musu wuta suna barci har suka kashe mutane akalla takwas.

'' Mun kwanta duk muna barci da yake an yi ruwa; sai kawai muka ji karar harbi. Mutane ne a gidan sun haura mutum dari, amma sai kowa ya shiga neman wurin buya'' Inji Muhammadu Ulama'u wani wanda ya tsira da ransa daga harin.

Karin bayani