Makamin kare dangi ya kusa tashi a Amurka

tashin bam din kare-dangi
Image caption Bayanin ya nuna yadda Amurka ke kusa da kusa da mummunan bala'i

Wani bam mai karfin gaske na Amurka da ya linka makaman kare dangi da aka jefa wa Japan sau 260 karfi ya kusa tashi a 1961 a North Carolina.

Wasu sabbin bayanai na sirri ne suka nuna hakan.

Wani jirgin yaki samfurin B-52 wanda ke dauke da bama baman ne ya lalace, a lokacin yana shawagi a sararin samaniyar garin Goldsboro.

Biyu daga cikin bama bamam sun fado daga jirgin kuma nan da nan daya ya fara shirin fashewa.

Bayan da ya fado kasa wani makunnin lantarki a jikinsa ya hana shi fashewa.