An kashe akalla mutane talatin a Kenya

Harin Kenya
Image caption Harin Kenya

Jami'an tsaro a Kenya sun ce, 'yan bindigar da suka yi ta harbe-harbe a wata cibiyar kasuwanci a babban birnin kasar, Nairobi, a yanzu an yi masu kofar-raggo a wani sashe na ginin.

Akalla mutane talatin sun hallaka, bayan da 'yan bindigar da suka rufe fuskokinsu, suka afka wa cibiyar cinikayyar. Wasu mutanen fiye da hamsin sun jikkata.

In ji wani wakilin BBC a Nairobin, ministan tsaron Kenyar ya gaya masa cewa, maharan sun yi garkuwa da wasu mutane.

Kungiyar Islama ta Al-Shabaab da ke Somaliya ta ce ita ke da alhakin kai harin.

Wani babban jami'in Al Shabaab din ya gaya wa BBC cewa, ramuwar gayya ce saboda kasancewar sojojin Kenya a Somalia.

Ma'aikatan majalisar dinkin duniya na kasashen waje da kuma jami'an diplomasiyya na zuwa sosai wannan cibiyar kasuwancin ta Nairobi.

Amurka ta yi alawadai da harin wanda wasu 'yan kasar suka jikata a ciki.