An yanke wa Bo Xilai daurin rai-da-rai

Image caption Bo xilai dai ya taba zama cikin jerin mutane 100 masu karfin fada-a-ji a duniya.

Wata kotu a kasar Sin ta samu tsohon babban jigon siyasar nan Bo Xilai da laifukan cin-hanci, da almubazzaranci da kuma anfani da mukami wajen aikata laifi.

Kotun wadda ke a birnin Jinan na lardin Shandong, ta yanke wa dan siyasar hukuncin daurin rai-da-rai; sai dai yana da damar daukaka kara.

Tsohon shugaban na jam'iyyar Kwaminis a lardin Chongqing dai ya musanta dukkan zarge-zargen lokacin da yake bada nasa bahasi gaban kotun a watan Agusta.

An dai sauke Bo daga mukaminsa ne a bara lokacin da aka samu wani abin fallasa da ya kai aka samu matarsa da laifin kashe wani dan kasuwar Burtaniya Neil Hollywood.

Karin bayani