Kasashen ECOWAS za su fara musayar bayanan tsaro

Image caption Kasashen dai na son maganin yadda wasu ke aikata laifi a wata kasa su gudu zuwa wata a yankin.

Ministocin tsaro na kasashen kungiyar ECOWAS sun amince jami'an tsaron kasashen su rika musayar bayanai da za su taimaka musu wajen farautar masu aikata laifuka.

Ministocin dai sun yi wani taro ne a Yamai ranar Assabar, domin duba matakan bai-daya da ya kamata su kara dauka domin tabbatar da tsaro a yankin na yammacin Afirka inda aka cika samun hare-haren mayakan sakai.

Kasashen 15 dai na fuskantar da matsalolin tsaro iri-iri, kamar ayyukan ta'addanci, da sace-sace, da safarar miyagun kwayoyi da makamantansu a 'yan shekarunan

Taron dai ya zo ne bayan shugabanin rundunonin 'yan sanda na kasashen kungiyar sun yi wasu taruka tsakaninsu tare da mika rahotanni ga ministocin tsaron.

Karin bayani