Angela Merkel ta sake cin zabe

Angela Merkel
Image caption Angela Merkel

Sakamakon farko na zaben majalisun dokokin Jamus ya nuna jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel ta sami gagarumar nasara.

Sai dai kuma ba za ta iya kafa gwamnati tare abokiyar kawancenta ta Jam'iyyar Free Democrats ba.

Jam'iyyar CDU ta sami kashi 42 cikin dari na kuri'un.

Dubban magoya bayan Jam'iyyar sun yi ta murna da tafi a Hedikwatar jam'iyyar, yayin da Angela Merkel ke jawabin godiya.