Yau ake zabe a Jamus

shugabar gwanatin jamus Angela merkel
Image caption Ana ganin za ayi kan-kan-kan a zaben Jamus

A ranar Lahadin nan ne masu zabe a Jamus ke kada kuria domin zaben 'yan mazalisar dokoki da kuma na shugabancin gwamnatin kasar.

Shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel na neman a sake zabenta a karo na uku.

A lokacin gangaminta na karshe Mrs Merkel ta shedawa magoya bayan ja'iyyarta ta Christian Democrat cewa zaben zai kasance kan-kan-kan.

Babban mai kalubalantarta Peer Steinbruek na jam'iyyar adawa ta Social Democrats ya bayyana gwamnatin da ke mulki a matsayin ta koma baya.

Ana dai tsammanin jam'iyyar Angela Merkel za ta yi nasarar samun kujerun majalisa da yawa.

Amma kuma wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar ta nuna cewa wata kila sai ta kai ga yin kawance domin kafa sabuwar gwamnati.