An rutsa 'yan bindiga a kenya

hari a cibiyar kasuwanci a Kenya
Image caption Al Shabaab ta ce ta kai harin ne saboda Kenya ta shiga rundunar sojojin kasashen duniya a Somalia

Jami'an tsaron Kenya sun ce sun rutsa 'yan bindigar da suka kai hari wata cibiyar kasuwanci a babban birnin kasar Nairobi.

Inda 'yan gwagwarmayar dauke da bundugogi suke rike da mutane da dama a kantin na Westgate Mall.

Kungiyar Al Shabaab ta Somalia ta ce ita ke da alhakin harin, wanda ya hallaka mutane 39 wasu 150 kuma suka sami raunuka.

Shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya ce akwai wasu daga cikin iyalansa da suka mutu a harin.