Musayar wuta a rukunin shagunan Kenya

Kenya
Image caption An dai kashe akalla mutane sittin da takwas.

An yi ta jin karar harbe-harben bindigogi da kuma fashewar abubuwa a rukunin shagunan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da mutane a Nairobi.

Ana tsammanin maharan tsakanin 10 zuwa 15, wadanda ake tunanin 'yan Kungiyar Al-Shabab ne, har yanzu na cikin ginin yayin da aka shiga rana ta uku da aukuwar lamarin.

Jami'an tsaro sun shaidawa BBC cewa an kubutar da mafiyawancin mutanen da harin da aka kai a rukunin shagunan ya rutsa da su.

An dai kashe akalla mutane sittin da takwas, an dai jikkata mutane 175 wadanda suka hada da Sojoji hudu, kuma suna samun kulawa a asibiti.

Karin bayani