An hana 'yan sabuwar PDP taro a Bauchi

PDP
Image caption Jam'iyyar PDP a Najeriya na fuskantar rikici

A jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, ana cece-kuce bayanda 'yan sanda suka hana taron sabuwar jam'iyyar PDP dake karkashin jagorancin Alhaji Abubakar Kawu Baraje.

Hukumomin tsaro a jahar ta Bauchi dai sun ce sun hana taron ne saboda batun rabewar jam'iyyar mai mulkin Najeriyar na gaban kotu, a saboda haka sai an jira an ga hukuncin da kotu zata yanke tukunna

Sai dai 'yan sabuwar PDPn na cewa wannan ba hujja ba ce tun da kotu bata hana gudanar da tarukan jam'iyya ba.

Ko a makonnin baya ma dai sai da jami'an tsaron Najeriyar suka rufe sakatariyar sabuwar PDPn a Abuja babban birnin kasar, lamarin da ya haifar da kace-nace.

Shugaban Najeriya dai ya gana da bangaren 'yan PDPn da suka balle a makon da ya gabata, a kokarin da ake na dinke barakar data sa jam'iyyyar ta dare gida biyu.

Karin bayani