An haramta kungiyar 'Yan Uwa Musulmi a Masar

Image caption Magoya bayan hambararren Shugaba, Muhammed Morsi

Wata kotu a Masar ta haramta dukkan ayyukan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta Masar.

An bukaci kotun ta sake nazarin matakin da aka baiwa kungiyar masu kishin Islama a watan Maris a matsayin kungiya mai zaman kanta.

Hukumomin soji a Masar sun kaddamar da ayyukan murkushe kungiyar tun bayan hambarrar da Shugaba Mohammed Morsi a ranar uku ga watan Yuli.

An tsare daruruwan 'yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi a Masar cikin hadda shugabbansu, Mohammed Badie, wadanda aka kamasu bisa zargin tada hankali da kisan kai.

Jami'an tsaro sun kashe daruruwan magoya bayan Mista Morsi wadanda ke kiran a maidodashi kan mulki.

Karin bayani