Kenya: Ana matakin karshe na fafatawa

Sojojin Kenya
Image caption Har yanzu ba a san inda mutane 63 suka shiga ba.

Jami'an Kenya sunce ana kan matakai na karshe domin kawo karshen fafatawar da ake yi tare da wadanda ake zargin mayakan kungiyar Al-Shabab ne a Nairobi

Tunda farko an ruwaito fashewar abubuwa da kuma harbe harben bindigogi , yayinda sojoji suka kutsa kai cikin ginin rukunin kantinan na Westgate.

Jami'ai sun ce an kashe 'yan ta'adda guda uku kuma sojoji na ci gaba da yiwa ginin kofar rago, suna dudduba mutanen da suka yi saura a cikin sa.

Jami'an hukumar agaji ta Red Cross sun fadawa BBC cewa har yanzu ba a san inda mutane 63 suka shiga ba.

Karin bayani