Dakarun Kenya sun kwace rukunin kantuna

Kenya
Bayanan hoto,

An kashe akalla mutane 62 a harin

Dakarun tsaron Kenya sun ce sun karbe iko da rukunin kantuna na Westgate a Nairobi, wanda 'yan bindiga suka kai hari, kuma aka kwashe kwanaki uku ana fafatawa.

An ji karar fashewar abubuwa da kuma aman wuta na fitowa daga ginin a ranar Talata da safe a yayin da akalla mutane 62 aka kashe tare da jikkata fiye da mutane 170.

Sai dai akwai fargabar cewa yawan wadanda suka mutu za su fi hakan, kuma an kashe uku daga cikin maharan.

Rahotanni dai na cewa jama'a na yin kaura daga yankin da abin ya faru, kuma kasuwar hannun jarin Kasar Kenyan ta fuskanci komabaya sakamakon wannan hari.