Ana ci gaba da fafatawa a Kenya

Harin Alshabab a Nairobi
Image caption Sojoji sun ce an kubutar da mafi yawan mutanen da aka yi garkuwa da su

Rahotanni daga Nairobi babban birnin Kenya sun bayyana cewa ana ci gaba da fafatawa tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindigar da suka yi garkuwa da mutane a rukunin kantunan Westgate.

Wuta na ci gaba da ruruwa a ginin, inda hayaki ya mamaye sararin samaniyar yankin.

Ministan harkokin cikin gida na kasar, Joseph Ole Lenku, ya shaidawa BBC cewa an kusa kawo karshen abin da ya kira matsalar da ake fuskanta.

Ya kara da cewa dakarun kasar sun kwace iko da dukkan benayen da ke cikin ginin.

Rahotanni na cewa an kashe akalla 'yan bindiga guda uku, kana aka ji wa wasu rauni.