Shugaba Obama ya yi tur da harin Kenya

Barack Obama
Image caption Obama ya dau alkawarin bada taimakon da ya zama wajibi

A kalamansa na farko na bainar jama'a a kan harin da aka kai a Nairobi, Shugaba Barack Obama na Amurka ya kira lamarin a matsayin wani abu mai matukar takaici.

Shugaban ya dau alkawarin bada taimakon da ya zama wajibi domin magance wannan bala'i.

Shi ma Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana damuwarsa , yana mai cewa aikin ta'addanci a Nairobi ya shafi kowa.

A Birtaniya Sakataren tsaro, Philip Hammond ya ce 'yan Birtaniya shida ne a yanzu aka yi imanin cewa an kashe.

Karin bayani