Guba ta kashe Giwaye 81 a Zimbabwe

Giwa a Zimbabwe
Image caption An tsare wasu masu farautar namun daji ba bisa ka'ida ba.

Jami'an kula da namun daji a Zimbabwe sunce giwaye 81 ne suka mutu, bayan da masu farautar namun daji ba bisa ka'ida ba, suka saka masu guba a wani gandun daji mafi girma na Zimbabwe.

Sanarwar ta biyo bayan wata ziyara da kwararrun gwamnati suka kai zuwa wani wurin shakatawa na Hwange a ranar asabar.

Wani jami'in sashen wurin shakatawar Jerry Gotora ya ce an saka gubar ta 'cyanide' wacce ake amfani da ita wajen hakar ma'adinin gwal a yankunan da giwayen suke kiwo.

An dai tsare masu farautar namun dajin ba bisa ka'ida ba su tara.

Karin bayani