Fyade: Maza 4 sun daukaka kara a India

Image caption Masu zanga-zanga a Delhi

Maza hudu wadanda aka yanke wa hukuncin kisa saboda laifin yi wa daliba fyade da kuma kashe ta a Delhi babban birnin India sun daukaka kara.

Mazan sun isa harabar babbar kotun Delhi cikin motar bus tare da rakiyar jami'an tsaro a yayinda masu zanga-zanga suka yi dafifi a gaban kotun.

Babbar kotun kasar za ta iya shafe watanni kafin ta soma sauraron karar a kan batun hukuncin kisan da aka yanke wa mazan su hudu.

A watan Disamba ne suka kaiwa buduwar hari, abinda ya janyo zanga-zanga a fadin India a kan batun sauya dokar fyade a cikin kasar.

Karin bayani