'Amurkawa da 'yar Ingila na cikin maharan Kenya'

Rukunin kantunan Westgate
Image caption Rukunin kantunan Westgate

Ministar harkokin kasashen waje ta Kenya Amina Muhammad ta ce akwai Amurkawa guda biyu da 'yar Birtaniya daya cikin wadanda suka kai hari a Nairobi.

Ministar ta ce Amurkawan matasa ne masu shekaru 18 zuwa kuma 19 a duniya 'yan asalin Somalia ko kuma Larabawa, amma sun zauna a Amurka a Minnesota dama wasu wurare.

Ta ce ita kuma 'yar Birtaniyar ta sha kai hare-hare a Kenya a baya.

Ta shaidawa manema labarai cewa akwai bukatar hadin kan sauran kasashen duniya, musamman ma Amurka da Birtaniya, saboda wanda aka kashe da wadanda su ka yi kisan 'yan asalin Kenya ne da Birtaniya da kuma Amurka.

Kungiyar AlShabab ta Somaliya ce ta dauki alhakin kai harin, a matsayin martani na tura sojojin Kenya zuwa Somaliya.