Dalibai sun yi zanga-zanga a jihar Legas

Image caption Malaman jami'oi na bukatar karin albashi da kyautata yanakin harkokin bincike a jami'oi

Dalibai a jihar Legas cibiyar kasuwancin Najeriya, na zanga-zanga a gaban Jami'ar jihar, domin neman gwamnatin Tarrayar ta sasanta da malaman jami'oi su koma koyarwa.

Daliban sun ce daga nan zuwa daya ga watan Okotoba, idan har gwamnatin Tarraya bata sasanta da malaman ba, to za su tabbatar abubuwa sun tsaya cik a birnin.

Malaman jami'oin kasar dai sun shafe kusan watanni biyu suna yajin aiki, bisa nuna rashin amincewa da kin cika alkawuran da gwamnatin kasar ta yi.

A baya dai gwamnatin ta sha alwashin kawo karshen yajin aikin malaman, amma hakan ya ci tura.