Persie ba zai buga wasa da Liverpool ba

Van persie
Image caption Robin Van Persie ya koma Manchester United ne daga kulob din Arsenal

Dan wasan gaba na Manchester United, Van Persie ba zai shiga taka ledar da kulob din zai yi da Liverpool a ranar Laraba ba, saboda raunin da ya samu.

Van Persie bai buga wasa a karawar da kulob din ya yi da Manchester City ba, inda aka lallasasu Manchester United da ci 4-1, a karshen sati saboda raunin da ya samu a mararsa.

Kocin Manchester United David Moyes ya tabbatar da cewa Van Persie ba zai buga wasa a karawar da za su yi a Old Trafford ba.

Ana sa ran Luis Suarez na Liverpool zai buga wasan na ranar Laraba, bayan dakatar da shi wasanni 10 da aka yi bisa cizon dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic.