Mutane fiye da 200 sun hallaka a Pakistan

Girgizar kasa a Pakistan
Image caption Daruruwan gidaje ne suka rushe

Adadin mutanen da suka rasu sanadiyyar girgizar kasar da ta afkawa kudu maso yammacin Pakistan a ranar Talata ya dadu zuwa fiye da dari biyu.

Mutane da dama kuma sun jikkata a girgizar kasar da ta faru a yankin Balochistan dake daura da iyakar Pakistan da Iran.

Daruruwan gidaje ne suka rushe yayinda dubunnan mutane suka kwana a waje.

An dai aika da agajin tantuna da magunguna zuwa yankin daga Quetta, babban birnin lardin.

Karin bayani