Riga kafi a Abuja saboda hari a Kenya

Image caption Jami'an tsaro a Najeriya

A Najeriya an tsaurara matakan tsaro a wasu cibiyoyin kasuwanci na wasu manyan biranen kasar da suka hada da Abuja babban birnin tarraya.

Hakan ya faruwa ne ganin irin abin da ya faru a Nairobi babban birnin kasar Kenya inda 'yan bindiga su ka yi kutse a wani babban kanti da ake kira Westgate Mall su ka yi garkuwa da daru-ruwan jama'a.

A bakin cibiyar kasuwanci ta Cedi Plaza dake Abuja, an jibge jami'an tsaro wadanda ke binciken ababen hawa masu kokarin shiga cibiyar don sayayya.

Wadanda wakilin BBC ya yi hira dasu a Cedi Plaza din sun ce basa fargabar komai duk da irin harin da aka kai a Kenya.

Karin bayani