Masu binciken makamai za su koma Syria

Masu binciken makamai na Majalisar Dinkin Duniya
Image caption Kasashen yamma sun dora alhakin kan gwamnatin Syria, yayin da Rasha ke zargin 'yan tawaye

Gwamnatin Rasha ta ce ana sa ran masu binciken makamai na Majalisar Dinkin Duniya, za su koma Syria ranar Laraba.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sergei Ryabkov ya ce masu binciken za su je gurare uku da ake zargin an kai harin makamai masu guba wato Khan al-Assal da Sheikh Maqsoud da kuma Saraqeb.

Masu binciken na shirin zuwa guraren, a lokacin da aka kai harin wajen garin Damascus a ranar 21 ga watan Agusta da ya kashe daruruwan mutane.

Rahoton majalisar dai ya ce an yi amfani da sinadarin Sarin a harin, ko da yake bai fito ya dora alhakin kan kowane bangare ba.