An soma jigilar mahajjata daga Ghana

Image caption Dakin Ka'aba a Makka

A birnin Accra na kasar Ghana an fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudi Arabia don gudanar da aikin Hajjin bana.

Maniyyata sama da dubu biyar ne ake saren za su gudanar da hajji bana a Saudi Arabia daga Ghana.

Hukumar dake kula da aikin haji a kasar ta Ghana ta ce ta kammala abubuwan da suka dace don maniyyatan su yi ibada a saukake.

Wasu daga cikin mata maniyyatan sun shaidawa wakilinmu na Accra, Iddi Ali cewar ba tare da muharrami za su tafi ba.

Karin bayani