Al'ummar Kenya na zaman makoki

Image caption Cibiyar kasuwanci ta Westgate da aka kai harin.

A kasar Kenya an soma makokin kwanaki uku domin alhinin rashin mutanen da harin masu kaifin kishin Islama ya rutsa da su a cibiyar kasuwanci ta Westgate dake birnin Nairobi.

Hukumomin kasar ta Kenya sun ce, mutane sittin da bakwai ne suka mutu, sai dai kuma akwai wasu mutanen da har yanzu ba a kai gano su ba.

Amma kungiyar Al Shabaab da ta kai harin tace, mutane dari da talatin da uku ne suka mutu, sai dai ba tantance hakan ba.

Kwararru masu bincike daga Amurka, da Isra'ila da Birtaniya suna aiki tare takwarorinsu na Kenya a wurin da aka kai harin domin zakulo sauran mutanen da lamarin ya rutsa da su.