Masu ciki sun koka da muzguna musu a asibiti

Mata 'yan Nijar da yaransu
Image caption Mata 'yan Nijar da yaransu

A Jamhuriyar Nijar, wasu mata masu ciki dake zaune a yankunan karkara na kokawa game da zargin muzguna musu da ake yi a lokutan awon ciki ko haihuwa.

Matan Agadez sun ce suna fuskantar kyara, hana su gadon kwanciya a lokacin da suka zo haihuwa.

Ana zargin likitoci da jami'an lafiya da aikata irin wadannan halaye ga mata masu ciki.

Sai dai likitocin sun ce fadan gyara kayanka su ke wa matan, domin da dama basa shirya wa haihuwar duk da cewa suna shafe watanni tara dauke da ciki.