Zanga-zanga kan farashin mai a Sudan

Image caption An kona tayoyi a kan titunan Khartoum

'Yan sandan Sudan sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Khartum dake nuna rashin amincewa da janye tallafin farashin mai.

Shaidu sun ce, masu zanga-zanga sun bankawa gine-ginen jami'a da kuma gidaje wuta, kuma suka rufe babbar hanyar zuwa filin jiragen sama.

Akalla mutane biyu aka kashe tun daga ranar Litinin lokacin da gwamnati ta janye tallafi akan farashin man petur.

Talakawan kasar na kallon matakin gwamnatin a matsayin alamar nuna rashin tausayi.

Karin bayani