Za a yanke wa Charles Taylor hukunci

Charles Taylor
Image caption An sami Taylor da laifin ta'addanci da fyade da amfani da yara a matsayin soji

Wata kotu ta musamman dake Hague dake samun goyan bayan Majalisar dinkin duniya zata zartar da hukunci akan karar da Tsohon Shugaban Liberia, Charles Taylor ya daukaka bayan da aka same shi da laifin aikata laifukan yaki a lokacin yakin basasa a Saliyo.

A bara ne Mr. Taylor ya zama tsohon Shugaban Kasa na farko da wata kotun kasa da kasa ta samu da laifin aikata laifukan yaki, tun lokacin shari'ar Nuremburg ta 'yan Nazi.

A watan Mayun shekarar 2012 ne wata kotu ta musamman ta yankewa Charles Taylor hukuncin zaman gidan yari na Shekaru hamsin.

An same shi da aikata laifukan yaki a Saliyo da suka hadar da ta'addanci da fyade da kisa da kuma amfani da kananan yara a matsayin soji.

Idan har bai samu nasara ba a karar daya daukaka, Charles Tailor zai yi zaman kurkuku a wani gidan yari dake kasar waje kuma Burtaniya na daya daga cikin Kasashe uku da suka amince zasu bada inda zai zauna.

Karin bayani