Kenya na neman 'yar Birtaniya ta cikin mahara

Samantha lewthwaite
Image caption An yi imanin Samantha na amfani da lakabin Natalie Webb

Hukumar 'yan sandan kasa da kasa na neman Samantha Lewthwaite, macen da ake zargin na cikin maharan da suka kai hari a rukunin shagunan Kenya.

Hukumar dai ta ce Kenya na tuhumar Samantha da laifin mallakar abubuwa masu fashewa da hada baki a shekarar 2011.

Samantha ta Musulta kuma ta auri wani dan kunar bakin wake da ya kai hari a layin dogo na London, shekaru takwas da suka wuce.

Ana alakanta matar wacce mijinta ya mutu, mai shekaru 29 da kungiyar Alshabab ta Somalia.